Connect with us

Labarai

Ambaliyar Ruwa: Sama Da Gidaje 16,000 Sun Lalace, Yayin Da Mutane 24 Suka Rasa Ransu

Akalla mutane 24 ne suka rasu tare da lalata gidaje 16,625 a jihar Katsina sakamakon ambaliyar ruwa da iska.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta ya sanya wa hannu a ranar Juma’ar nan ya ce adadin gonaki 1,620 ne ruwa ya mamaye a kananan hukumomin Danja, Ingawa da Kafur na jihar.

Ya ce amfanin gona da aka kiyasta an yi asara yakai miliyoyin naira sakamakon bala’in.

Muhammad ya bayyana cewa hukumar ta tantance gidaje da gonakin da abin ya shafa domin taimakawa wadanda abin ya shafa.

Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar za ta fara rabon kayan agaji ga wadanda abin ya shafa.

Gidan Talabijin na Channels  ya ruwaito a ranar 5 ga watan Satumba, 2022 cewa, gidaje 3,813 sun lalace tare da mutuwar mutane biyar sakamakon ruwan sama da aka yi a wasu kauyuka a Katsina.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet