Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jihar Kano Ta Yabawa Shirin KN-CARES Wajen Gyaran Hanyoyi

Kwamishinan Kasafi da tsare-tsare na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Danazumi Gwarzo ya yaba da kokarin da shirin KN-CARES ke yi na gyara hanyoyin karkara da suka lalace tsawon kilomita 90 a fadin jihar.

Dan’azumi ya bayyana cewa kokarin gyara hanyoyin cikin watanni 4 cikin gaggawa abin yabawa ne.

A cewarsa, Wannan kokarin ya zo daidai da shirin Gwamna Ganduje na gyaran hanyoyin karkara mai taken Karkara Salamu Alaikum.

Kwamishinan ya yi kira ga manoma da su yi amfani da hanyoyin jigilar abinci da aka gyara, tare da ba da hadin kai ga shirin na KN-CARES, wajen daukar shirye-shiryen noma daban-daban da nufin inganta wadatuwar abinci.

Kwamishinan ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya duba wasu hanyoyin a kananan hukumomin Gwarzo, Karaye da kuma Rogo, wadanda shirin tallafawa manoma da masu kananan karfin na KN-CARES.

Hanyoyin da shirin ya gyara sun hada da Zango – Butawa a Gwarzo, Bariki – Yar Madaka – Unguwar Maye da Barkono – Karshi a cikin Rogo da Kwanar Gaye – Taiki a Karamar Hukumar Karaye.

Kwamishinan ya kara jaddada kyakkyawar aniyar gwamnatin jiha na gyara manyan hanyoyin jigilar abincin, ta yadda za a samu saukin jigilar kayayyaki da ayyuka daga wuraren da ake nomawa zuwa kasuwanni.

Bugu da kari, yayin da yake gudanar da zagayen kwamishinan, hadi da mai kula da ayyukan KN–CARES na jiha, Alhaji Muntari Ado Yakasai ya sanar da kwamishinan cewa, an gyara tsawan kilomita 90 daga cikin lalatattun hanyoyi a kananan hukumomi 18, ta hanyar aikin tun farkon watan Mayun 2022.

Jami’ar yada labarai ta shirin, Shafa’atu Sa’id Karaye, cikin wata Sanarwa da ta aikewa da jaridar Dimokuradiyya ta ce Gyaran hanyoyin a yankunan karkara na daya daga cikin muhimman abubuwan da shirin KN-CAERES ke da shi na ci gaba da inganta isar da kayayyakin amfanin gona, da kuma samar da ayyukan noma zuwa yankunan karkara da fitar da amfanin gona zuwa kasuwanni.

A jawabinsa a wajen taron, shugaban gudanar da shirin na jihar Kano Mal Rufa’i Halilu ya yi kira ga al’ummar da suka amfana da su kafa kwamitocin kula da hanyoyi da za su samar da gyare-gyaren da ya kamata idan bukata ta taso.

Bugu da kari, Malam Rufa’i ya kuma horas da manoma kan kiyaye kiyaye hanyoyin amfani da hanyoyin, da kuma kula da itatuwan da aikin ya shuka ta yadda za a samu yanayi mai kyau da zai sanya ƙarko ga hanyar.

A nasu jawabin godiya, wakilai Mal Ubale Batuwa, Alhaji Maharazu Hassan Na Bello da Nafi’u Bashiru Rogo na kananan hukumomin Gwarzo, Karaye da Rogo, sun godewa gwamnatin jiha da kuma shirin KN – CARES Project bisa ceto su a lokacin da suke bukata.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet