Connect with us

Labarai

Ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PRP ya naɗa Suhaib Auwal kakakin yaƙin neman zaɓensa

Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PRP Salihu Tanko Yakasai da ake kira da Ɗawisu, ya naɗa Suhaib Auwal Gwagwarwa a matsayin jami’in yaɗa labarai na yaƙin neman zabensa.

Naɗin nasa na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun dan takarar na jam’iyyar PRP wadda kuma aka raba wa manema labarai a Lahadin nan.

A cewar sanarwar, Matashi Suhaib kwararren ɗan jarida ne a fannin aikin gidan Talabijin da Rediyo har ma da aikin jarida na kafar Internet da kuma kafafen sada zumunta na zamani.

Suhaib ya fara aikin jarida ne a gidan rediyon Freedom na Kano, kana ya zama mai ɗakko rahoto kuma kodinetan yada labarai na zamani.

Haka kuma ya yi aiki a tashar talabijin ta Liberty da ke Kaduna a matsayin mai tace labarai da hotuna masu motsi watau Video editing.

Suhaib ya kuma yi aiki da wasu kafafen yaɗa labarai na kafar Internet da suka haɗa da Solacebase da Daily News 24.

Har zuwa naɗin nasa, Suhaib yana aiki da tashar talabijin ta tauraron ɗan Adam mai suna Gaskia TV wadda ke ƙasar Ghana a matsayin mataimakin shugaban ofishin Kano, tare da aiki da gidan Rediyon Premier a matsayin mai ba da shawara kan kafofin yaɗa labarai na zamani.

Sabon kakakin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan na PRP ya yi nasarar kammala karatun digiri na biyu a fannin aikin jarida daga Jami’ar Igbinedion a Okada da ke Jihar Edo, kuma ya halarci kwasa-kwasai da sauran nazarce-nazarce da kwasa-kwasai da dama a ciki da wajen Najeriya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvmarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasibomcasibomjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasibomgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet