Labarai
Allah ya yi wa Ɗan majalisa mai wakiltar Bakori rasuwa a Madina
Ɗan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar ƙaramar hukumar Bakori Dakta Ibrahim Aminu Kurami ya rasu a kasar Saudiyya.
Rahotonni sun bayyana cewa, dangin marigayin sun ce, ya rasu ne sakamakon gajeriyar jinya a Madina da misalin ƙarfe biyu daren jiya a agogon Najeriya.
Haka kuma sun ƙara da cewa ɗan majalisar dai ya je ƙasar mai tsarki ne domin yin aikin Umrah.
Marigayin Dakta Ibrahim Aminu, ya rasu ya bar mata biyu da ƴaƴan goma sha da jikoki uku.
An dai zaɓe shi ne a matsayin ɗan majalisar dokokin a zaɓen cike gurbi da aka gudanar ranar 31 ga watan Oktoban shekerar 2020 bayan rasuwar wanda ya gada Alhaji Abdurrazak Ismail Tsiga.
AHF
