Lafiya
Fiye da ƴan Afirka Miliyan 116 ne ke fama da matsalar ƙwaƙwalwa- WHO
Hukumar lafiya ta duniya watau WHO, ta bayyana cewa, fiye da mutane miliyan ɗari da goma sha shida ne ke fama da lalurar ƙwaƙwalwa a nahiyar Afirka.
Daraktar hukumar a Afirka Dakta Matshidiso Moeti, ce ta furta hakan yau Litinin a birnin tarayya Abuja a saƙon ta bikin ranar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa ta duniya na bana.
Haka kuma ta ce, Taken na bana ya zama abin tunatarwa bayan kusan shekaru uku, warewar zamantakewar al’umma da kare kai daga cutar COVID-19 har ma da sauran matsalolin tattalin arziki.
Ta kuma ce, nahiyar Afirka na buƙatar ɗaukin gaggawa wajen daƙile matsalar tu’ammali da barasa a tsakanin matasa musamman ƴan ƙasa da shekaru goma sha uku da ke yawan hallaka kansu ko kuma su kamu da lalurar ƙwaƙwalwa.
Taken bikin ranar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwar na bana shi ne “Samar da lafiyar ƙwaƙwalwa da jin dadi ga kowa a faɗin duniya”.
