
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya isa ƙasar Chadi a yau Litinin domin halartar bikin rantsar da Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar ƙasar na tsawon shekaru biyu.
BBC ta ruwaito ce, yanzu haka ana gudanar da bikin rantsuwar ne a N’Djamena babban birnin ƙasar.
Haka zalika za a tattauna kan batun mayar da ƙasar turbar dimukraɗiyya, bayan mutuwar tsohon shugaban ƙasar Idriss Deby Itno.
