Featured
Champions League: Messi ya fice daga tawagar da za ta fafata da Benfica
Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa
Lionel Messi baya cikin tawagar ‘yan wasan Paris St-Germain da za su kara da Benfica a gasar cin kofin zakarun Turai na yau Talata saboda raunin da ya ji.
Messi, mai shekaru 35, ya zura kwallo a fafatawar da suka yi a Portugal a makon da ya gabata, kafin daga bisani aka cire shi.
Har ila yau, dan wasan na Argentina, bai buga karawar da suka tashi kunnen doki da Reims a gasar Ligue 1 ranar Asabar ba inda PSG ta gaza samun nasara a gasar a karon farko a bana.
PSG ce ke kan gaba a rukunin H da maki bakwai, inda Benfica ke biye mata, sai Juventus ta uku.
