Kasuwanci
Majalisar Dokokin Kano Ta Karbi Rahoton Yadda Gwamnati Ta Kashe Kudi A 2021
Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi rahoto kan yadda gwamnati Kano ta kashe kudi a shekarar 2021 data gabata.
Majalisar ta karbi rahotan ne a zamanta na Talatar nan karkashin shugabanta injiniya Hamisu Ibrahim Chidari.
Babban mai binciken kudi na gwamnatin Kano Isma’il Bala, ne ya aikewa da majalisar rahoton domin bibiya tare da yin nazari akai.
Bayan karbar kundin bayanan ne kuma majalisar ta baiwa kwamitin ta dake kula da dukiyar al’umma karkashin dan majalisa mai wakiltar Doguwa Salisu Ibrahim Muhammad domin yin nazari da gabatar da rahotansa nan da watanni uku masu zuwa.
Haka zalika majalisar ta amince da dokar sauyawa jami’ar kimiya da fasaha ta Wudil suna zuwa jami’ar kimiya da fasaha ta Aliko Dangote wato (Aliko Dangote University of Science and Technology Wudil.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Labaran Abdul Madari ya kuma ce yanzu komai na jami’ar zai koma dauke da sunan Aliko Dangote.

gate io
07/06/2023 at 8:00 pm
The point of view of your article has taught me a lot, and I already know how to improve the paper on gate.oi, thank you. https://www.gate.io/pt-br/signup/XwNAU