Connect with us

Featured

Za Mu Sauya Salon Mulkin Da APC Ta Sanya Jama’ar Kasar Nan — Atiku

Dan Takarar Shugabancin kasa na jam’iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin sauya mugun halin da jam’iyyar APC ta sanya jama’a a dalilin salon mulkin ta.

Atiku ya yi wannan alkawari ne a garin Uyo na jihar Akwa Ibom a wajen kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na 2023 a jam’iyyar PDP a ranar Litinin.

Wazirin Adamawa wanda ya jaddada kudirinsa na ceto Najeriya daga mummunan shugabancin da jam’iyyar APC ta shimfiɗa, ya tunatar da cewa a lokacin da PDP ta yi mulki, kasar ta fi dacewa a dukkan bangarorin rayuwar kasa fiye da yadda ake samu a halin yanzu.

Ya ce, “Jam’iyyar APC ta gaza a kasar nan ta kowane fanni da suka hada da tsaro, tattalin arziki, da ilimi da sauransu.

“A lokacin da PDP ke mulki, ‘yan Najeriya sun san kwanciyar hankali da tattalin arziki, kuma batun rashin tsaro bai yi muni ba kamar yadda muke da shi a yanzu.

“Don haka ne muke yakin neman ceto kasar nan daga mummunan shugabancin da APC ta kai mu.

Dole ne mu kubutar da Najeriya domin a fili yake cewa ba za mu iya sake baiwa jam’iyyar APC damar kara kai mu kan turbar da ta sanyamu ba.

“Dole ne mu dawo da jam’iyyar PDP a lokacin zabe domin PDP ce kadai jam’iyyar siyasa da ta tabbatar da gaskiya da kuma iya sauya mugun halin da APC ta gindaya.

“Aiki mafi mahimmanci a gaban shugaban kasar nan na gaba shi ne hada kan kasa kuma babu wani daga cikin ‘yan takara a wannan zabe da zai iya yin ikirarin yin hakan fiye da ni da kuma ka’idojin shigar da jam’iyyar PDP,”

A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya ce jam’iyyar za ta shiga wannan kamfen a matsayin kungiya daya.

Ayu ya kara da cewa, “Tsarin jirgin na PDP ya motsa kuma yayin da jirgin ya bar tashar, za mu shirya tsaida jirgin domin daukar sabbin mutane wadanda, ko wani dalili, ba sa nan tare da mu a yau.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet