Featured
Barcelona zata fafata da Inter Milan a Champions League
Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa
A Yau Laraba Barcelona za ta karbi bakuncin Inter Milan a wasa na hudu a cikin rukuni na uku a Champions League da za su kara a Camp Nou.
Ranar Talata 4 ga watan Oktoba, Inter Milan ta yi nasara a kan Barcelona da ci 1-0 a fafatawar da suka yi a San Siro.
Wannan shi ne wasa na 16 da za su kara a gasar zakarun Turai, bayan da Barcelona ta yi nasara a takwas da canjaras hudu, Inter Milan ta ci uku daga ciki.
Bayern Munich ce ta daya a rukuniin mai maki tara, sai Inter Milan da maki shida, Barcelona maki uku ne da ita da kuma Viktoria Plzen, wadda ba ta da maki.
Tuni kociyan Barcelona, Xavi ya bayyana ‘yan wasa 21 da zai fuskanci kungiyar Italiya.
‘Yan kwallon sun hada da Ter Stegen, Piqué, Sergio, O. Dembélé, Pedri, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Marcos A., Jordi Alba, Kessie, S. Roberto, F. De Jong.
Sauran sun hada da Raphinha, Eric, Iñaki Peña, Balde, M. Casadó, Gavi, Pablo Torre and Arnau Tenas. Out through injury are Bellerín, R. Araujo, Memphis, Christensen da kuma Kounde.
