Labarai
Gwamnatin Ganduje ta zargi ƴan Kwankwasiyya da ƙwacen wayoyin mutane
Gwamnatin jihar Kano ta yi Allah-wadai ga wasu magoya bayan tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Engr Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP bisa zargin su da tada zaune tsaye tare da ƙwacen wayoyin mutane yayin ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar wanda Kwankwaso ya yi a Sharada.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai Malam Muhammad Garba ya fitar a yau Alhamis.
Sanarwar ta bayyana cewa, yayin da gwamnati ke tabbatar da dai-daiton filin yakin neman zabe na dukkan jam’iyyun siyasa, abin takaici ne yadda jam’iyyar ta NNPP ta fara kai hari ga jama’a da basu ji ba basu gani ba.
Haka kuma ta cikin sanarwar Kwamishinan yaɗa labaran na jihar Kano, Ya ce, ya kamata taron ya zama na lumana, sai dai wasu cikin mambobin jam’iyyar sun yi amfani da muggan makamai tare da riƙa afka wa ƴan ba ruwa na lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu da kuma sace wayoyin mutane.
Malam Garba ya ƙara da cewa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, ta yi matuƙar kaɗuwa ganin cewa da alama akwai wani yunƙuri da jam’iyyar NNPP ta yi da gangan na wargaza yanayin siyasar da ake fama da shi a jihar Kano.
Haka kuma ya ce, Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ɗora wa jami’an tsaro alhakin ci gaba da gudanar da ayyukansu ta hanyar tabbatar da cewa duk wani gangamin siyasa ya zamanto cikin kwanciyar hankali tare da tunkarar duk wani mutum ko ƙungiyar da ke shirin haifar da rikici.
