Ilimi
Gwamnatin Kaduna Ta Shirya Jarabawar Daukar Sabbin Malamai
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana ranar 17 ga watan oktoba domin fara tiwa sabbin Mlmalamai 10, 000 Jarabawa daukar aiki.
Hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna KADSUBEB ta bayyana cewa, ta shirya gudanar da jarabawar daukar malaman makaranta daga ranar 17 zuwa 28 ga watan Oktoba a shiyyoyi uku na jihar
Sanarwar da KADSUBEB ta fitar ta ce za a gudanar da jarrabawar ne a cibiyar fasahar sadarwa ta Kofar Doka, Zariya; Harabar Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) da ke Kaduna da kuma reshen KASU a Kafanchan, mai wakiltar shiyyar Arewacin jihar, Tsakiya da kuma Kuduncin jihar ta kaduna.
A watan Yuli, Shugaban Hukumar ta KADSUBEB, Malam Tijani Abdullah, ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya bukaci hukumar ta dauki malamai 10,000 a jihar.
