Connect with us

Labarai

Ma’aikatan Muhalli Sun Gano Wani Mutum Da Aka Kulle Shekaru 20 A Wani Gida

 

‘Yan sanda suka ceto wani dattijo mai shekaru 67 da aka kulle a daki sama da shekaru 20 a Kaduna ranar Larabar nan.

An gano mutumin ne tsirara kuma an kulle shi a wani daki a wani gida da ke hanyar Bayajidda a cikin garin Kaduna.

Mazauna ginin sun gudu a lokacin da tawagar ‘yan sanda suka isa gidan.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN cewa za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Jalige ya ce wasu jami’an kiwon lafiya na muhalli da ke karkashin karamar hukumar Kaduna ta Arewa ne suka fara gano mutumin mai suna Ibrahim Ado, wadanda ke cikin gidan.

A cewar wani ganau, jami’an kula da muhalli sun ziyarci gidan a yau domin duba wasu abubuwan sha da aka ajiye a gidan amma sun gano wani mutum a kulle a daki.

A cewar majiyar, sun kulle shi kusan shekaru ashirin.

“Sun kai rahoto ga sashin ‘yan sanda na Magajin Gari, kuma kwamishinan ‘yan sanda ya umurci jami’ai da su kwashe wanda abin ya shafa.

“Ya kuma ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin don bayyana al’amuran da suka shafi lamarin da kuma dalilin da ya sa aka kulle mutumin na tsawon wannan lokaci,” in ji shi.

Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Jalige ya ce an kai wanda abun ya sjafa asibiti domin a duba lafiyarsa.(NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet