Siyasa
Jam’iyyar APC ta buƙaci INEC ta sanya Machina a matsayin ɗan takatar Sanatan Yobe ta Arewa
Jam’iyyar APC ta buƙaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC kan da sanya Bashir Machina a matsayin ɗan takatar Sanatan mazaɓar Yobe ta Arewa.
Jam’iyyar ta buƙaci hakan ne ta cikin wata wasiƙa da ta aike wa hukumar tana mai cewa ta yi hakan kasancewar babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta ayyana shi a matsayin halastaccen ɗan takara.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Takardar wadda shugaban jam’iyyar na ƙasa Abdullahi Adamu da Sakataren ta Sanata Iyiola Omisore suka sanya wa hannu, sun buƙaci hukumar da ta buga sunan Machina kamar yadda kotu ta bada umarni.
A cewar sanarwar “Muna mai sanar da hukumar zabe mai kwanan wata 28 ga Satumba 2022, da kuma oda mai kwanan wata 5 gawatan Oktoba 2022, daga babbar kotun tarayya da ke Damaturu, inda muke umartar hukumar ta amince da Machina a matsayin dan takarar jam’iyyar na Sanatan Yobe ta Arewa”.
