Labarai
Kano- Kotu ta ɗaure matashiyar da ke yin sojan gona da kakin ƴan sanda
Kotu Ta Yankewa Matashiyar Dake Yin Sojan Gona Da Kayan Ƴan sanda A Kano Hukunci
Kotun majistirit mai lamba 54 Karkashin jagorancin mai Shari’a Mansur Ibrahim Yola, ta yankewa wata matashiya mai suna Zainab Salisu Ishaq mazauniyar unguwar Sheka Baranda hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan ajiya da gyaran hali ko zabin tarar naira dubu hamsin.
Ana dai tuhumar Zainab ne da laifin yin sojan gona a cewar ita jami’ar yar sanda ce ta kwantar da tarzoma, wanda hakan ya sabawa sashi na 319 na kundin penal court.
Tun da fari, wani Jami’in ɗan sanda ne mai suna ASP Iliyasu Umar ya kamata lokacin da yake gudanar da aikinsa akan titin sabon gari zuwa New Road by court Road, inda ya ganta sanye da uniform din mobile police mai mukamin inspector tana tsaye akan titi tana bada hannu.
Jami’in kotun Muhammad Haruna Zakirai ya karanta tare da fassara mata kunshin tuhumar, inda nan ta ke ta amsa laifin ta.
Sai dai ta bayyana cewa sha’awa aikin yake bata shi yasa ta sanya kakin na ƴan sanda.
Mai gabatar da kara lauyan gwamnati Barista Aminu Kawo ya nemi da ayi mata hukunci nan ta ke tunda ta amsa laifinta.
Daga karshe, kotun ta yanke mata hukunci ɗaurin watanni shida a gidan ajiya da gyaran hali ko zabin tarar naira budu hamsin.
