Connect with us

Labarai

Zargin satar kuɗaɗe: Hukumar EFCC ta cafke ma’aikatan banki su 12

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta ce, ta cafke wasu ma’aikatan banki su goma sha biyu bisa zargin su da satar kuɗaɗe a bankuna da suke aiki a Jihar Enugu.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a ƙarshen makon nan.

Sanarwar ta ce, binciken farko da hukumar ta fara gudanarwa ya gano cewa waɗanda ake zargin sun saci kuɗaɗe daga wasu asusai da ba sa aiki a wani daga cikin reshen bankunan da a yanzu ba sa aiki.

Haka kuma ta ce, “An tura kuɗaɗen ne daga asusan da ke rufen zuwa mutane daban-daban, kuma tuni EFCC ta gano wanda ya fi kowa samun rabo mai tsoka na kuɗin.”

Cikin mutanen goma sha biyu akwai mata huɗu da kuma maza takwas.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da: Odeniyi Anthony da Deki Kingsley Onyekachi da Oguchukwu Ene da Elendu Chizaram sai Anyakora Uchenna da Onah Kingsley da kuma Akwe Elizabeth.

Sauran su ne, Chinenye Grace Acibe da Victoria Ezedie da Chidi-Ukah Obinna sai Etoh Lawrence Uzochukwu da kuma Udeze Harrison.

Haka kuma hukumar ta EFCC, ta ƙara da cewa za ta gurfana da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar ta kammala bincike a kansu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet