Labarai
Jiragen Nigerian air za su fara aiki kafin ƙarshen shekera- Shugaba Buhari
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce ana sa ran jiragen sama na Nigerian air za su fara aiki kafin ƙarshen shekarar nan da muke ciki.
Shugaban ya bayyana hakan ne yau Litinin a birnin tarayya Abuja yayin da yake bayyana bude taron sake duba ayyukan ministoci karo na uku da aka shirya domin tantance ci gaban da aka samu wajen aiwatar da manufofin gwamnatinsa.
Haka kuma ya ƙara da cewa, ana ci gaba da gudanar da aikin ne tare da bayar da takardar shidar tabbatar da filayen jiragen sama na Lagos da Abuja daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya yayin da filayen jiragen Kano da Fatakwal ke gudanar da irin wannan tsarin ba tare da shaidar ba.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Shugaba Muhammadu Buhari, ya kuma shaida wa mahalarta taron da kuma manyan baƙi da suka halarci taron da suka haɗa da tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta cewa an gina sama da kilomita dubu uku da ɗari takwas na hanyoyi a faɗin Najeriya, yayin da aka sayo sabbin jiragen sama talatin da takwas ga rundunar sojojin sama domin inganta aikin yaƙi da ƴan tada ƙayar baya.
