Connect with us

Labarai

Gwamnatin Zamfara ta nemi afuwa kan rufe wasu kafofin yaɗa labarai da ta yi

Gwamnatin Zamfara ta nemi afuwa kan rufe kafofin yaɗa labarai da ta yi da suka haɗa da NTA da Pride FM Gusau da wasu sauran guda uku.

Hakan dai na cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Alhaji Ibrahim Dosara ya fitar yau Talata.

Tun da fari dai gwamnatin ta zargi kafafen yaɗa labaran da ta rufe ɗin da karya dokar zartarwa mai lamba 10 tare da cin zarafin aikin jarida.

Sauran tashoshin sun haɗa da: Gamji TV da Gamji FM da kuma Al-umma TV.

Solacebase ta ruwaito cewa, Dakta Abdullahi Shinkafi, jigo a jam’iyyar APC mai mulkin jihar kuma shugaban kwamitin shari’ar ƴan fashi da muggan laifuka na jihar ya miƙa saƙon neman afuwar yayin da yake zantawa da manema labarai a Gusau babban birnin jihar.

Ya kuma ce, “wamnati ta fusata ne bisa zargin karya dokar zartarwa mai lamba 10, 2022, wacce ta fara aiki a ranar 13 ga Oktoba.”

“A cikin wannan oda, gwamnati ta haramta duk wani gangamin siyasa da tarukan siyasa a jihar saboda matsalar tsaro, tare da dakatar da duk wasu shirye shiryen siyasa a jihar tare da rufe hanyoyin a kananan hukumomin Anka, Bukuyum da Gummi baki daya da sauran garuruwa da kauyukan da abin ya shafa, ” Inji Dakta Abdullahi Shinkafi.

Haka kuma ya ƙara da cewa, “Kafafen yaɗa labaran da abin ya shafa sun karya dokar ne ta hanyar halartar gangamin taron siyasa na ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP Dakta Dauda Lawal-Dare a Gusau ranar Asabar ɗin da ta gabata.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet