Labarai
Neja: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Likita tare da majinyata a harin da suka kai asibiti
Wasu ƴan bindiga da ke ɗauke da muggan makamai, sun yi garkuwa da Likita tare da majinyata da dama a harin da suka kai asibitin Abdulsalam Abubakar da ke a yankin ƙaramar hukumar Lapai ta jihar Neja.
Rahotonni sun bayyana cewa ƴan bindigar sun kuma hallaka mutane biyu tare da yin garkuwa da fiye da mutane goma da suka haɗa da likitoci biyu da marasa lafiya.
Haka kuma wasu rahotonnin sun ce, lamarin ya faru ne da tsakar daren wayewar yau Talata.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa guda cikin waɗanda ɓata garin suka kashe tsohon jami’in lafiya ne.
