Labarai
Tinubu Da Shattima Sun Gana Da Shugabannin Arewa A Jihar Kaduna
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima a halin yanzu suna ganawa da shugabannin yankin arewacin kasar nan a karkashin inuwar kungiyar hadin gwiwa ta Arewa domin yin wani zaman tattaunawa.
Taron dai wani bangare ne na tattaunawa da zababbun ‘yan takarar shugaban kasa domin tattauna shirinsu ga yankin, gabanin babban zaben kasar na 2023.
Fitowar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC na zuwa ne kwanaki biyu bayan da abokin hamayyarsa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi irin wannan ganawa da shugabannin na Arewa.
Gamayyar kungiyoyi shida daga Arewa ne suka shirya taron tattaunawa a gidan Arewa dake Kaduna wanda suka hada da Arewa Consultative Forum, Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation, Northern Elders Forum, Jamar Matan Arewa da dai sauransu.
Taron dai wani bangare ne na shawarar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya dauka na janyo hankulan dukkan bangarorin al’ummar Najeriya da sakon yakin neman zabensa na hadin kan kasa da kuma ci gaban kasa.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Tinubu yana tare da Babban Daraktan Majalisar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na APC da Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong da Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi, Edward Onoja.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir-El-Rufai da takwarorinsa na Nasarawa, Abdullahi Sule, Atiku Bagudu (Kebbi), Abubakar Badaru (Jigawa), Mai Mala Buni (Yobe), Babajide Sanwo-Olu (Lagos) da Bello Matawalle (Zamfara). sun kuma halarci taron.
Sauran manyan baki da suka halarci taron sun hada da tsohon gwamnan jihar Zamfara, kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, shugaban kungiyar tuntuba ta Arewa, Cif Audu Ogbeh, shugaban kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi da wasu da dama daga cikin shugabannin arewa.
