Labarai
Tinubu- Zan ɗora a kan irin kyawawan manufofin shugaba Buhari
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a zaɓen baɗi Bola Ahmed Tinubu, ya ce, idan ya karɓi mulkin Najeriya zai ɗora ne a kan salon jagorancin mulki irin na shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Bola Tinubu, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga mahalarta taron duba ayyukan ministoci karo na uku a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja jiya Talata.
Haka kuma,ya ce, gwamnatinsa za ta duƙufa wajen cigaba da ayyukan Buhari; musamman ayyukan da ya gada da nufin samar da wadata ga ƴan kasa.
Ya kara da cewa manufofin na sa za su ta’allaka ne ga samar da kyakkyawan tsarin gudanar da mulki da gyara al’ummar kasa.
Tinubu, ya kuma ce, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi ƙoƙari wajen magance tashe-tashen hankula ya yi wa Boko Haram illa sosai tare da shawo kan lamarin.
