Wasanni
U-17: Najeriya ta je zagayen dab da na kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya
Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa
Tawagar kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya Flamingos, ta samu nasarar kaiwa wasan dab da na kusa da na karshe, a gasar lashe kofin duniya ‘yan kasa da shekaru 17 da ke gudana a kasar India.
Tawagar dai ta samu gurbin ne bayan da ta doke takwarar ta, ta Chile a wasan karshe na rukunin B da ci 2 da 1, wanda ya bata damar hada maki 6.
A yanzu dai Flamingos zata kara ne da takwarar ta, ta Amurka a ranar Juma’a wacce ta kare wasan rukunin A a matsayin ta daya.
Wasan dai zayyiwa Flamingos tsauri ganin yadda ta zura kwallaye 13 a gasar kuma aka sanya mata kwallo daya rak.
Wannan ne dai karo na farko da Flamingos ke kokarin kaiwa ga matakin kusa da na karshe a gasar, yayinda itama Amurka ke wannan runkuri a karo na biyu tun bayan da aka fara gasar a shekarar 2008 da ta kare a mataki na biyu.
