Kasuwanci
Gwamnatin tarayya ta umarci kamfanonin Sadarwa su janye ƙarin kashi 10 na kiran waya da suka yi
Gwamnatin tarayya, ta umarci kamfanonin Sadarwa su janye ƙarin kashi 10 na kiran waya da suka yi a baya-bayannan.
Hukumar kula da kafafen sadarwa NCC ce ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da kwanan watan 12 ga wannan watan da muke ciki na Oktoba wadda daraktan hulɗa da Jama’a na hukumar Dakta Reuben Muoka, ya sanya wa hannu.
A cewar hukumar an ɗauki matakin ne biyo bayan rahotonnin da kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa na aiwatar da tsarin bai daya na kashi goma cikin ɗari da aka amince wa kamfanonin Sadarwar a baya-bayannan.
Haka kuma ya ce, an ɗauki matakin ne bayan dogon nazari musamman kan yanayin aiki da yanayin kasuwanci a Najeriya, domin ya shafi dukkan bangarorin tattalin arziki.
