Labarai
Ogun: Wata Kotu Ta Yi umarnin A Sake Zaben Fidda Gwani Na Takarar Majalisar Wakilai
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abeokuta, jihar Ogun, ta umarci jam’iyyar PDP da ta gudanar da sabon zaben fidda gwani na mazabar Abeokuta ta Arewa da Obafemi-Owode da Odeda.
Kotun ta kuma bayar da umarnin cewa dole ne jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) su kula da sabon zaben fidda gwanin.
Wanda ya shigar da karar, Abiodun-Oni Samuel Oluwafemi, ya ja jam’iyyar PDP, shugaban PDP na kasa; Iyorchia Ayu, shugaban jam’iyyar PDP na jihar; Sikirulahi Ogundele, da INEC a gaban kotu, a matsayin wadanda ake tuhuma na 1, 2, 3 da 4, yana kalubalantar sakamakon zaben fidda gwani.
Mai shigar da karar ta bakin lauyansa, A. Okelola, ya caccaki jerin sunayen wakilan da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaben fidda gwanin.
Da yake yanke hukuncin, mai shari’a J.O Abdulmalik ya umarci jam’iyyar da ta sake gudanar da sabon zaben fidda gwani na mazabar tarayya ta Abeokuta North/Obafemi-Owode da Odeda a cikin kwanaki 14 daga ranar da aka yanke hukuncin.
Kotun ta kuma ba da umarnin cewa dole ne jam’iyyar ta yi amfani da jerin sunayen wakilai na asali don sake zaben, inda ta kara da cewa dan takarar da ya fito sabon zaben fidda gwani ya kamata INEC ta amince da shi.
Da yake mayar da martani, lauyan mai shigar da kara, A. Okelola ya yabawa bangaren shari’a kan tsayawa kan turbar gaskiya da adalci.
Ya ce a karkashin tsarin dimokuradiyya, dole ne a samar da daidaito a kuma bai wa kowa damar shiga ba tare da tauye hakkin kowa ba, kuma a gode wa Allah bisa tsarin shari’a wanda a kodayaushe yake kare duk wani buri.
Shima a nasa martani, mai shigar da karar ya godewa bangaren shari’ar bisa damar da aka ba shi na kwato masa hakkinsa, yana mai tabbatar da cewa yana da tabbacin samun nasara a duk lokacin da za a sake zaben.
“Na yi imani da wannan hukuncin a yanzu, batutuwan jerin sunayen karya da na kangaro da aka gudanar a ranar 22 ga watan Mayu 2022 za su zama tarihi,” in ji shi.
