Labarai
NSCDC Ta Kama Wasu Mutane Biyar Bisa Zargin Satar Kayan Wutar Lantarki
Jami’an hukumar tsaro mai kula da fararen hula (NSCDC) sun kama wasu mutane biyar da suka kware wajen lalata wayoyin wutar lantarki da taransfoma a unguwar Pambegua da ke karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a shedikwatar hukumar da ke babban birnin jihar Kaduna, Kwamandan NSCDC a jihar, Idris Adah, ya ce mutanensa ne suka kama su a lokacin da suke gudanar da wannan aikin wani sintiri na yau da kullun a Pambegua.
A cewarsa, wadanda ake zargin sun amsa laifin lalata wata na’urar taransifoma a babban asibitin Pambegua, sannan kuma sun sace wayoyi masu sulke na wata taransfoma kafin jami’an NSCDC su cafke su.
An kuma gano wasu abubuwan baje koli daga wadanda ake zargi da suka hada da satar wayoti masu sulke da fitulun titi.
Kwamandan NSCDC ya ce sauran wadanda ke da hannu a wannan aika-aika suna nan a hannunsu, kuma ragowar mutanen suna bin sa da nufin cafke su, yayin da wadanda ake tuhuma biyar da aka kama zuwa yanzu za a gurfanar da su gaban kotu idan an kammala bincike.
Sai dai ya yi gargadin cewa Kaduna ba za ta sake zama mafakar masu barnatar da dukiyar gwamnati da na jama’a ba, domin rundunar ta ci gaba da fafatawa da duk wanda aka samu da aikata irin wannan laifi da rashin kishin kasa.
