Labarai
Gwamnatin Matawalle ta buɗe wasu Kasuwanni da hanyoyi da ta rufe a baya
Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Bello Muhammad Matawalle, amince da buɗe wasu kasuwanni da hanyoyi da ta rufe a baya sakamakon matsalar tsaro.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanawar da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Alhaji Ibrahim Dosara ya sanya wa tare da raba ta ga manema labarai.
Sanarwar ta ce, gwamnatin jihar ta amince ne da buɗe wasu kasuwanni da kuma manyan hanyoyin ƙananan hukumomin jihar da suka haɗa da na Gummi da Anka da kuma Bukkuyum.
Haka kuma sanarwar ta buƙaci al’umma da su kasance masu bin doka da oda.
