Labarai
Niger: Hukumar FRSC Ta Tabbatar Da Jikkatar Mutane 21 A Wani Hatsarin Mota
Hukumar kiyaye aukuwar hadura ta kasa (FRSC) a Nijar ta ce mutane 21 ne suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Bida zuwa Minna ranar Lahadin nan.
Mista Kumar Tsukwam, Kwamandan sashin, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN a ranar Litinin din nan a Minna cewa hatsarin ya afku ne da misalin karfe 9:25 na safe kusa da kauyen Sabon Gida a karamar hukumar Bida.
Ya bayyana cewa hatsarin ya hada da wata mota kirar Toyota Bus mai lamba NSR 540 ZG da wata mota kirar Range Rover mara rijista.
A cewarsa, mutane 21 ne hatsarin ya ritsa da su kuma dukkansu sun samu raunuka daban-daban.
Ya ce 14 daga cikin wadanda suka jikkata an kai su Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya ta Bida, yayin da sauran bakwai kuma aka kwashe su zuwa babban asibitin Umaru Sanda da ke Bida domin yi musu magani.
Kwamandan sashin ya ce hatsarin ya afku ne a lokacin da daya daga cikin tayoyin motar kirar Toyota ta cire, sannan motar ta daki babbar motar Range Rover da ke tafe.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa, Ya shawarci masu ababen hawa da su yi taka-tsan-tsan, su rika duba ababen hawansu yadda ya kamata kafin su hau kan hanya sannan kuma su bi tsauraran matakan da za su bi don guje wa hadurra.
