Labarai
Wasu Jiga-jigan Jam’iyyar PDP A Sokoto Sun Koma Jam’iyya Mai Mulkin Kasa
Alhaji Garba Tozai, mataimaki na musamman ga Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, da Garba Araga, mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Isa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Masu sauya shekar sun koma APC ne tare da dimbin magoya bayansu, kamar yadda wata sanarwa da Bashar Abubakar, mai baiwa Sanata Aliyu Wamakko shawara kan harkokin yada labarai ya fitar a Sokoto jiya Asabar.
Abubakar ya ruwaito tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP, wanda ya yi magana a madadin sauran wadanda suka sauya sheka na cewa sun yanke shawarar ne la’akari da martabar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar.
“Bugu da kari, da Alhaji Ibrahim Lamido a matsayin dan takarar Sanata na jam’iyyar APC na shiyyarmu, babu shakka za a share mana hawaye,” in ji shi.
Araga ya kuma yabawa Wamakko, da shugaban jam’iyyar APC a jihar, ya kuma yi alkawarin hada kai tare domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023.
A wani labarin kuma, jam’iyyar ta samu dimbin ‘yan jam’iyyar PDP da suka sauya sheka a garin Gadanbe da ke yankin Katami ta Kudu a karamar hukumar Silame.
Da yake karbar sabbin mambobin, mai rikon jam’iyyar APC na yankin, Alhaji Dalhatu Dantama, da wani jigo, Alhaji Abubakar Rana, sun ba su tabbacin cewa za a yi masu adalci daidai da sauran ‘ya’yan jam’iyyar.
