Labarai
LASEMA Ta Ceto Mutane 7 Da Suka Makale A Gobarar Da Ta Tashi A Hukumar WAEC
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) ta ceto mutane bakwai daga wata gobara da ta tashi a shedkwatar hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) da ke jihar Legas.
LASEMA da safiyar ranar Larabar nan ta ce lamarin ya fara ne sanadiyyar “wutar lantarki”.
Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce, “Da isar wurin da aka ambata, an gano wani sashe na babban bene na shedikwatar ta WAEC yana cin wuta.
“Binciken da aka yi ya nuna cewa gobarar ta tashi ne a hawa na 3 na bene mai hawa 12 sakamakon wutar lantarki.
“Jimillan mata bakwai ma’aikatan Hukumar sun makale a hawa na 5 da na 7 kuma an kwashe su cikin koshin lafiya saboda gaggawar da tawagar ceto ta yi. Haka kuma an kashe wutar gobarar kuma.”
An tattaro cewa wasu daga cikin ma’aikatan sun samu raunuka a yayin da suke tserewa daga ginin.
Sanarwar ta ce ana ci gaba da tantancewa lamarin bala’i da kuma adadin ma’aikata.
“Haɗin gwiwar tawagar hukumar tare da ma’aikatan lafiya na hukumar, LASG FIRE, FED FIRE, UNILAG FIRE, LASAMBUS, da LASTMA suna nan a ƙasa don tabbatar da samun murmurewa cikin gaggawa.” Inji LASEMA. “Aikin farfadowa yana gudana.”
