Featured
Ronaldo ya yi atisaye da ‘yan wasan Manchester United
Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Cristiano Ronaldo ya koma atisaye cikin abokan wasansa bayan umarnin da mai horas da kungiyar Erik ten Hag ya ba shi.
Ronaldo mai shekaru 37, ya ki tsayawa a sanya shi a wasan da kungiyar ta buga da Tottenham a Larabar da ta gabata, lamarin da ya sanya aka ciri shi daga jerin ‘yan wasan da suka fafata da Chelsea a ranar asabar inda suka buga 1-1.
Ten Hag ya ce dole ne Ronaldo ya girbi shukar da yayi ta rashin da’a
Toh amma sai dai bayanai sun tabbatar da cewar dan wasan sun tattauna da mai horas da kungiyar a cikin ‘yan kwanakin nan
