Labarai
Ba Za Muyi Sakaci Da Rahotonnin Amurika Da Birtaniya Ba — Minista
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba da rahotannin ta’addanci da gwamnatocin Amurka da Birtaniya suka fitar.
A cewarsa, Najeriya ba za ta yi wani sakaci da duk wani abu da wata gwamnati ta shawarceta kan al’ummarta da ke zaune a Abuja da sassan kasar nan ba.
Ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata, jim kadan bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Mohammed ya bayyana cewa Amurka ta sauke hakkinta na ba ‘yan kasarta shawarar su koma gida amma irin wannan gargadi ko mataki ba zai sanya Najeriya guiwarta yai sanyi ba.
Ya jaddada cewa, a ‘yan watannin da suka gabata gwamnati ta dauki kwakkwaran mataki na tsaro, inda ya bukaci ‘yan kasar nan da su guji yada abubuwan da ka iya tada hankulan jama’a
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai kasashen Amurka da Birtaniya suka yi gargadin yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a Abuja, musamman a gine-ginen gwamnati da wuraren ibada da makarantu da sauran cibiyoyi da jama’a suka taru.
Amurka ta kuma bukaci ‘yan kasarta da ma’aikatan ofishin jakadancinta da ke babban birnin Tarayya Abuja dake Najeriya da su fice daga kasar.
Amma ma’aikatar kula harkokin wajen ta kasa ta bukaci mazauna Abuja da ma ‘yan Najeriya baki daya da su kwantar da hankalinsu, tana mai cewa jami’an tsaro za su ji da lamarin.
