Connect with us

Labarai

Mista Geng Quangrong ya musanta zargin hallaka marigayiya Ummita 

Mista Geng Quangrong ɗan asalin ƙasar Sin da ake zargi da hallaka tsohuwar budurwarsa Ummukhulsum Sani Buhari da aka fi sani da Ummita, ya musanta zargin cewa shi ne ya kashe ta.

Ɗan kasuwar ya musanta hakan ne bayan da aka sake gurfanar da shi a gaban kotu a yau Alhamis.

BBC ta ruwaito cewa, Bayan karanto masa zargin a babbar kotun Kano, Mista Geng Quangrong ya ce, zargin da ake yi masan ba gaskiya ba ne.

Haka kuma ta ruwaito cewa, Mista Guo Cunru, shi ne mutumin da ofishin jakadancin China a Najeriya ya turo don ya yi wa wanda ake zargin tafinta daga turancin Ingilishi zuwa harshen Chinanci.

Lauya mai gabatar da kara wanda kuma shi ne kwamishinan Shari’a na Kano, Musa Abdullahi-Lawan, ya bukaci kotun ta fara sauraren tuhumar da ake yi wa wanda ake zargin.

Alkalin babbar kotun Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 16 ga watan gobe na Nuwamba domin gabatar da shaidun da masu kara suka za su kawo.

Idan za a iya tunawa dai, Ana zargin Mista Geng da kutsa kai cikin ɗakin Ummita tare da caka mata wuƙa a gidansu da ke unguwar Jan Bulo da ke Kano a watan Satumba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet