Labarai
Fadakarwar Ta’addanci: UK Ta Sanar Da Shawarar Tafiye-tafiye Ga Yan Birtaniya A Abuja
Ofishin Harkokin Waje, Kasashe rainon Ingila da cigaban Burtaniya (FCDO) ya sabunta shawararsa na balaguro ga ‘yan Burtaniya a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, FCDO ta shawarci “a kan duk wani balaguro zuwa babban birnin tarayya, har da cikin birnin Abuja.”
Ya kara da cewa “akwai barazanar kai harin ta’addanci a Abuja. An shawarci ‘yan Burtaniya da su kasance cikin faɗakarwa, su guji tafiye-tafiye marasa mahimmanci a cikin birni kuma su bi labaran cikin gida da shawarwarin hukumomin tsaro.
“Ofishin diflomasiyyar Biritaniya ya kasance a bude don muhimman ayyuka. Za a ci gaba da bitar shawarwarin tafiye-tafiye don tabbatar da cewa ta yi daidai da halin da ake ciki a Abuja da Najeriya.”
Tun da farko, FCDO ta ba da shawarar balaguron tana mai baiwa jama’arta shawara da su “yi la’akari da motsi a hankali, bin labaran cikin gida da shawarwarin hukumomin tsaro”.
Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa, Amurka ta ba da irin wannan shawara duk da cewa gwamnatin Najeriya ta baiwa jama’a tabbacin kare lafiyarsu.
“Shawarwarin balaguron FCDO ya kasance don sanar da ‘yan Burtaniya don su yanke shawara game da yin balaguron,” in ji sabuwar shawara daga gwamnatin Burtaniya.
“Sauran jihohin Najeriya da muke ba da shawara kan duk wata tafiye-tafiye masu mahimmanci, sun hada da Bauchi, Kano, Jigawa, Niger, Sokoto, Kogi, Abia, Plateau, Taraba, da ke tsakanin kilomita 20 daga kan iyakar Niger a jihar Kebbi da kuma yankunan da ba na kogin Delta ba, jihohin Bayelsa da Ribas.”
