Connect with us

Labarai

Kano: Magidanci ya rasa ransa sakamakon faɗawa rijiya

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar rasuwar wani magidanci Malam Habibu Mu’azu mai shekaru arba’in da biyar a garin ƴan dutse da ke yankin ƙaramar hukumar Bichi.

Jami’in hulɗa da jami’a na hukumar Saminu Yusuf Abdullahi, ne bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a.

Sanarwar ta ruwaito cewa jami’an hukumar ƙaramar hukumar ta Bichi ne suka karɓi kiran gaggawa da misalin ƙarfe 07:44 na safe daga wani mai suna Malam Sanusi Abubakar inda ya sanar da su faɗawa Rijiyar da mutumin ya yi.

Haka kuma ta cikin sanarwar jami’in ya ce, “Bayan isar jami’anmu wurin da misalin ƙarfe 8:20 na safe, sun fito da shi ba ya cikin hayyacin sa, kuma bayan kai shi asibiti likita ya tabbatar da rasuwarsa.”

“Tuni hukumar mu ta miƙa gawarsa ga dagacin garin na Ƴan Dutse Malam Bello Usman, kuma muna ci gaba da binciken musabbabin faruwar lamarin, Inji mai magana da yawun hukumar ta kashe gobara ta jihar Kano.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet