Labarai
Gwamnatin Gombe Ta Dauki Ma’aikatan Lafiya 440 A Jihar
Gwamnatin jihar Gombe ta dauki ma’aikatan kiwon lafiya 440 aiki domin sake fasalin fannin da ingantaccen aiki.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan hulda da manema labarai na gidan gwamnatin Gombe Ismaila Misli a ranar Asabar din nan.
Ya ce jami’an da aka dauka aikin sun hada da Ugozoma 106, Ma’aikatan Lafiyar Jama’a 213 (CHEW), Kananan Ma’aikatan Lafiyar Jama’a 132 (JCHEW) wadanda za a tura su cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko a fadin Jihar.
“Saboda gwamnatin yanzu ta Gwamna Inuwa Yahaya ta yi imanin cewa kiwon lafiya a matakin farko shine tushen tsarin kiwon lafiya,” in ji shi.
Ya bayyana cewa gwamnati mai ci ta ba da fifiko ga harkokin kiwon lafiya da walwalar ‘yan jihar, don haka aka samu dimbin jari a bangaren.
Ya ce daukar ma’aikata wani babban abin alfahari ne a tarihin wannan fanni a jihar, baya ga fara aikin gida a asibitin kwararru, da hada hadar kwararrun masu ba da shawara.
Misili ya ce fara hora da ci gaba da gina sabuwar kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma da ke Gombe duk sun yi nisa ne domin inganta aikin dan Adam na kiwon lafiya a jihar. (NAN)
