Labarai
Munguno Ya Ce Babu Wani Abun Fargaba, Ga ‘Yan Najeriya
Dangane da shawarwarin tsaro na baya-bayan nan da Amurka da Burtaniya suka bayar, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Babagana Monguno, ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa babu wani abin fargaba.
NSA, ya ce an shawo kan lamarin, ya bayyana abun a matsayin karya da rashin da’a na rashin tsaro a Abuja kamar yadda Birtaniya da Amurka suka fada.
Monguno ya bayyana hakan ne a ranar Litinin din nan a wani taro bayan taron majalisar tsaro da shugaban kasa Muhamadu Buhari ya jagoranta a fadar gwamnati.
Ya dage cewa fadakarwar ta kasance ga ƴan ƙasar Amurka da Biritaniya kuma yadda aka fitar da shi ya dagula al’amura.
Monguno ya shawarci ‘yan Najeriya da su rika gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba, inda ya ce jami’an tsaro ne ke da iko, kuma kasa Najeriya na da tsaro.
Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; Babban Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ahmed Abubakar, da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya); Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola; da kuma ministan harkokin ‘yan sanda, Mohammed Dingyadi.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Babban hafsan tsaron kasa, Janar Lucky Irabor ya jagoranci hafsan hafsoshin da suka hada da babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; Shugaban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Isiaka Oladayo Amao ga taron.
