Labarai
Shugaba Buhari ya taya Luiz Inácio Lula da Silva murnar lashe zaɓen shugaban ƙasa
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya taya sabon zaɓaɓɓen shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva murnar lashe zaɓen da aka gudanar a ƙasar.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kan kafafen yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar a yau Litinin.
Sanarwar ta ruwaito cewa, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi fatan sabon shugaban na Brazil zai ƙarfafa alaka tsakanin ƙasarsa da Najeriya.
Sabon shugaban ya samu nasara ne a kan abokin hammayarsa Jair Bolsonaro wanda har yanzu bai amince da shan kaye ba kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC ta ruwaito.
