Connect with us

Labarai

Wata Amarya Ta Mayarwa Da Ango Sadaki Da Lefe, Bayan Wata Guda Da Aure

A ranar Litinin din nan Wata kotun shari’a da ke zamanta a Magajin Gari, Kaduna, ta umurci wata matar aure, Maryam Dahiru da ta mayar da sadaki Naira 100,000 da akwatunan tufafin da ta karba daga hannun tsohon mijinta Salihu Yakubu.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Malam Rilwanu Kyaudai, ya tabbatar da rabuwar aure tsakanin ma’auratan ta hanyar Khul’i (saki ta hanyar yarjejeniya).

“Kawai za ta mayar da tufafin da bata ruga ta yi amfani da su ba, Mai karar ta kuma bukaci izinin Kotu da ta kwashe kayanta daga gidan tsohon mijin nata.” A cewar mai shari’an.

Tun da farko, Maryam Dahiru, ta bakin lauyanta Murtala Gyallesu, a ranar 12 ga watan Oktoba ne ta shigar da kara a gaban kotu inda take rokon kotu ta raba auren da suka yi wata daya ta hanyar Khul’i.

Ta ce yanzu ba ta da sha’awar auren, kuma a shirye take ta mayar da sadakin da ta karba domin a raba auren.

A nasa bangaren, Yakubu ta bakin lauyansa, M. M. Dahiru, ya ce yana son matarsa ​​kuma ba shi da niyyar sakinta.

Yakubu ya roki kotu da ta umarci tsohuwar matarsa ​​da ta mayar da akwatunan auren da aka cika mata su da kayan da ya ba ta. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet