Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA, ta ce, ta cafke mutum ɗari da talatin ɗauke da miyagun ƙwayoyi a jihar Kaduna a watan da muka yi ba kwana da shi na Oktoba.
Shugaban hukumar a jihar ta Kaduna Umar Adoro, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Laraba.
BBC ta ruwaito cewa shugaban na NDLEA ya kuma ce, bakwai daga cikin mutanen mata ne, inda ƙwayoyin aka kama suka kai kimanin Kilogiram 1,728.536.
Haka kuma ya ce, hukumar ta rushe wurare ashirin waɗanda suka yi ƙaurin suna wajen hada-hadar miyagun ƙwayoyi a jihar.
Umar Adoro ya kuma ce miyagun kwayoyin da hukumar ta ƙwace sun haɗa da ganyen wiwi kilogram 1,388.811 da hodar Iblis ta kilogram 0.019 da heroin kilogram 0.001 da ƙwayoyin Tramadol mai nauyin kilogram 7.666 sai wasu nau’in kwayoyin da nauyinsu ya kai kilogram 331.786 da kuma miyagun magungunan maye da ake harhaɗawa da nauyinsu ya kai kilogram 0.253.
