Connect with us

Labarai

Wata Kotu Ta Bayar Da Umarnin A Kamo Kwamishinan Ayyuka

Babbar Kotun Majistare da ke zamanta a Uke, a karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa, ta bayar da sammacin cafkewa tare da tsare Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na Jihar, Idris Mohammed, a gidan yari da ke Keffi.

Mohammed ana tuhumar sa da laifin hada baki da cin hanci da rashawa a karar da wani Injiniya Idris Aliyu Bori daya shigar a kan sa.

Ana tuhumar Kwamishinan ne tare da wasu mutane biyar da kutsawa cikin kasar wadanda suka kai karar, inda suka haddasa barna da kuma tsoratar da su.

Bayan rashin halartar Kwamishinan a Kotu, Lauyan wanda ya shigar da kara, Eunice Emmanuel Esq, ya roki belin da aka ba shi tun da farko a soke shi tare da bayar da sammacin cafkewa mai laifi don nuna dalilin da ya sa ya kamata kar a rasa jinginar belin.

Mai shari’a A’isha Abdullahi a hukuncin da ta yanke ta amince da bukatar lauyoyin masu korafin tare da bayar da umarnin a kamo Kwamishinan nan take.

An dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Nuwamba, 2022.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet