Connect with us

Labarai

‘Yan Najeriya Ba Su Da Wani Dalilin Yin Korafi Akan Yunwa, In Ji Buhari

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ‘yan Najeriya ba su da wani dalili na yin korafin yunwa a lokacin da kasar ta samu albarkar filayen noma.

Buhari ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da wani gidan talabijin na Tambari Hausa wadda aka watsa a daren ranar Laraba.

A yayin da yake amsa tambaya kan yadda ake fama da yunwa a kasar, shugaban ya ce duk wanda yake jin yunwa da gaske zai debi kayan aikinsa ya nufi gona.

A cewarsa, rufe iyakokin kasa da sauran manufofin da gwamnatinsa ta bullo da su don tabbatar da samar da abinci ya haifar da sakamako mai kyau.

“Idan kuna kokarin kawo min rahoto ga ‘yan Najeriya cewa ban cika alkawari ba, bari in tambaye ku, lokacin da na hau ofis, ban bayar da umarnin rufe iyakokin kasa ba har kusan shekaru biyu?” .

“Na dauki wannan matakin ne na dakatar da shigo da shinkafa, na ce mu noma abin da muke ci ko kuma mu mutu da yunwa.

“Na ce tunda muna da filin noma kuma Allah ya albarkace mu da ruwan sama, wane dalili ne dan Najeriya zai ce yana jin yunwa? Idan kana jin yunwa ka tafi gona.”

Da yake karin haske, shugaban ya ce: “Ina sane da cewa ambaliyar ruwa ta lalata wasu gonaki a bana amma har yanzu muna sayar da shinkafar da aka yi a Najeriya, kuma za mu iya ciyar da kanmu. Shin wannan ba nasara ba ce?

“Muna da ma’aikatan da suka bar ofisoshinsu na na’urar sanyaya dakj suka shiga noma, kuma sun sami girbi mai yawa. Don haka muna godiya.”

Akan yaki da cin hanci da rashawa, shugaban ya kuma ce an samu nasarori da dama.

Jaridar DailyNigerian ta rawaito cewa, Da aka tunatar da cewa har yanzu cin hanci da rashawa na ci gaba da bunkasa a cikin gwamnatin sa, Mista Buhari ya kalubalanci wadanda ke da sahihiyar shaida da su gabatar da shi ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet