Labarai
Kwankwaso Ba Kashin Yarwa Bane, Rigima Yanzu Aka Fara – Alhassan Doguwa
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta tarayya Alhassan Ado Doguwa ya ce Kwankwaso ba abin yarwa bane a Kano.
A cewarsa in dai mutum zai fadi tsakani da Allah ya san cewa Kwankwaso a matsayin sa na gwamnan, yayi aikin da kowa ya yaba.
A jawabin da ya gabatar ga magoya bayansa a daren yau Juma’a Doguwa ya ce, Duk Ɗan Kano ƙarya yake yace Kwankwaso bai yi rana ba.
Doguwan ya kuma yi zazzafan martani ga mataimakin Ɗan Takarar Gwamnan Jam’iyyar APC a Kano Alhaji Murtala Sule Garo.
A cewar shugaban masu rinjayen ba za su yi shi ba, kuma rigima tsakaninsa da Murtala yanzu a ka soma.
