Labarai
Gwamnatin Kano ta magantu kan rahoton Sahara Repoters
Gwamnatin Jihar Kano tayi martani game da wani rahoto da kafar yada labarai ta Sahara Reporters ta
wallafa, wadda ta bayyana cewa Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje yana daga cikin gwamnonin
da aka samu makudan kudade a gidajensu.
Kwamishinan yada labarai na jįihar Kano kwamarade Muhammad Garba ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Muhammad Garba ya ce labarin ba shi da tushe ballantana makama don haka al’umma su yi watsi
da shi.
Ya kara da cewa bayan sanarwa da hukumar EFCC ta fitar a kan wasu Gwamnoni 3 da tace tana sanya idanu
akansu, bata bayyana sunan gwamnonin ba.
To amma jaridar Sahara Reporters ta kama sunan gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda
kuma hakan ya saba da ka’ida.
Muhammad Garba ya ce wajibi ne Jaridar ta nemi yafiyar Ganduje bisa abinda ta wallafa wanda ba gaskiya ba ne.
