Connect with us

Labarai

NEMA Ta Rarraba Kayan Agaji Ga Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa

 

Ofishin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA reshen jihar Adamawa, ya raba kayan abinci da sauran kayayyakin agaji ga gidaje 800 da aka gano a matsayin wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2022 a karamar hukumar Madagali ta jihar.

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Hafiz Bello, kuma aka rabawa manema labarai a Yola ranar Lahadi.

A cewarsa, kayayyakin sun hada da daruruwan buhunan shinkafa, wake, masara, galan na man kayan lambu,da tumatur da sauran su.

Sauran abubuwa kuwa sun hada da tabarmar roba, tawul, barguna, gidajen sauro, kayan sawa kamar rigar yara, rigar maza, bokiti, faranti, cokali da kofunan robobi.

Alhaji Mustapha Habib, Babban darakta na hukumar, wanda ya samu wakilcin shugaban ayyuka, Mista Ladan Ayuba, a wurin rabon kayayyakin, ya ce matakin nuna damuwa ne ga wadanda abin ya shafa.

Ya kuma yi kira ga wadanda abin ya shafa da su yi amfani da kayayyakin da suka dace domin samun taimako da kwanciyar hankali daga bala’in da ya same su a lokacin damina.

Ya yi nuni da cewa, kimanin kananan hukumomi 433 a cikin jihohi 35 na tarayyar kasar nan ne ambaliyar ta shafa.

“Bari in yi amfani da wannan dandalin don sake yin kira ga ‘yan Najeriya da su daina yin gine-gine kan hanyoyin ruwa ko kuma zama a wuraren da ruwa ke gudana,” in ji shi.

Ya shawarci ‘yan Najeriya da su bi Alamomin Gargadi na Farko, EWS, daga Hukumar Kula da Ruwa ta Kasa da sauran hukumomin da abin ya shafa suka bayar don kare kansu daga fadawa cikin ambaliyar ruwa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet