Connect with us

Labarai

Hukumar FRSC Ta Karyata Amfani Da Na’urar POS Wajen Karbar Tara

Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa, ta bayyana cewa, Ba ta Amfani da na’urar cire kudin tafida gidanka wato POS Don Karbar Biyan Tarar masu ababen hawa da suka karya ka’idojin hanya.

Jami’in kula da ilimantar da jama’a na hukumar FRSC, Bisi Kazeem ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa a da ya fitar ranar Laraba.

A cewar sa, na’urar da Jami’an hukumar ke amfani da ita wacce ake kira da Corps’ Electronic Booking Device (E-Tablet) da aka kera don bayar da tikitin ga masu ababen hawa, an bata sunan ta zuwa na’urar PoS.

Kazeem ya kuma bayyana cewa Jami’an hukumar ba ta amfani, kuma ba ta ba da izinin amfani da na’urar POS ba kuma ba ta karɓar kuɗin tarar laifuffukan ta hanyar amfani da na’urar a wuraren sintiri.

Ya bayyana cewa, E-Tablet wani bangare ne na kokarin bullo da fasaha a cikin ayyukan Hukumar da kuma “kashe amfani da takardar yin rajista wanda hanya ce ta hannu ta ajeyi bayanan masu laifi da aka maye gurbinsu tsarin da na’urar ta hanyar fasahar zamani

A cewar Kazeem, bullo da na’urar ya bada gudun mawa wajen inganta tattara bayanai masu karfi da kuma hanzarta tattara bayanan masu laifi a cikin kundin adana bayanai na kasa.

Ya kara da cewa, na’urar daya ce kuma an yi ta ne domin tantance lasisin tuki na kasa da lambar motar da sauran kayayyaki da aiyukan kiyaye hadurra na kasa

Kazalika, Mukaddashin Rundunar, Dauda Ali Biu, ya nanata cewa, ya kamata jama’a su lura da cewa hukumar ba ta amfani da na’urar POS sai dai na’urar tantance tikiti wato E-Tikect wanda a halin yanzu ke kara samar da saukin ga harkokin hukumar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet