Labarai
Wasu Jagororin Jam’iyyar Hamayya A Yobe Sun Koma Jam’iyar APC Mai Mulki
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni Ya tarbi Hajiya Musafaram tsohuwar jagora a Jam’iyar PDP da ta sauya sheka daga jam’iyar zuwa APC mai mulki a Jihar.
Daraktan Janar na yada labarai da kula da harkokin kafafen yada labaran Gwamnan Mamman Mohammed ne ya bayyana hakan acikin wata sanarwa da ya fitar.
Ta sanarwar ta bayyana cewa, Hajiya Musafaram wacce jigoce a Jam’iyar PDP, wacce ta dade a jam’iyar tun a shekarar 1999 ta dawo Jam’iyar APC Mai Mulki
Da take jawabi, Hajiya ta bayyana cewa, Ayyukan Gwamnatin Bunina bunkasa rayuwar al’ummar jihar ne ya sanyata ta sauya sheka zuwa APC .
Kazaljka Gwamna Buni ya kuma tarbi tsohon Mamba a Majalissar Zartaswa ta Jam’iyar PDP a Karamar hukumar Geidam zuwa jam’iyar APC mai mulki.
Gwamnan ya tabbatarwa Sabbin Mambobin Jam’iyar APCn cewa, za su sami dama kamar yadda Sauran ya’yan jam’iyar APCn suke samu.
