Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce, sojin sama sun kai farmaki maɓoyar wasu ƴan ta’adda da suka yi garkuwa da wasu mutane tare da fatattakar ƴan bindigar da kuma lalata sansanonin su.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana faruwar lamarin ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce, jami’an rundunar sojin saman Najeriya sun gudanar da farmakin ne ta sama a wasu yankuna na jihar.

Haka kuma Samuel Aruwan a sanarwar ya bayyana cewa a yankin Kawara da ke karamar hukumar Igabi, an gudanar da sumame kan wani gungun ƴan bindiga.

“An samu nasarar hallaka ƴan bindiga su uku kuma wasu daga cikin wadan da aka yi garkuwa da su sun tsere daga yankin gaba daya”.

Haka kuma ya ce, a ƙaramar hukumar Chikun ma, an gudanar da aikin a yankunan Faka da Kangon Kadi da Damba da Ungwan Turai da Galbi da Gwagwada da wasu yankunan da dama a karamar hukumar lgabi.

Aruwan ya bayyana cewa an rufe hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da yankunan da ke kusa da su irin su- Buruku, Labi, Udawa, Manini da Polewire har zuwa Kajuru, Jaka da Rabi da Maguzawa.

“Za a ci gaba da sintiri na kasa da na sama a wadannan wurare da sauran wurare,” in ji Aruwan.