Labarai
Rundunar Yan Sanda Ta Gargadi Jam’iyyu da Yan Siyasa Wajen Amfani da Yan Banga
Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta gargadi ‘yan siyasa kan daukar ‘yan daba domin samun kariya a zaben 2023 mai zuwa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Haruna Garba ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da ‘yan sandan suka shirya domin tunkarar zaben 2023.
Kwamoshinan ‘yan sandan ya ce dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima ta amince da ‘yan sanda da hukumomi ‘yan uwanta ne kawai a matsayin wadanda aka ba su damar samar da tsaro a duk lokacin aikin.
Don haka Kwamishinan ya yi gargadin cewa duk wani dan siyasa da aka samu da makami a lokacin zaben za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.
Garba ya kuma shawarci jam’iyyun siyasa da su guji zage-zage, kalaman kyama da kuma nuna sha’awar rikici.
A cewarsa, “Babu wani buri da ya kai jinin kowa; idan aka kayar da kai, za ka iya yin nasara a nan gaba.”
Kwamishinan ya ce ‘yan sandan sun shirya tsaf domin samar da isasshen tsaro domin tabbatar da an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
CP ya kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa da su mika jadawalin yakin neman zaben su ga ‘yan sanda domin yin kyakkyawan shiri.
Shima da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan zabe na hukumar zabe mai zaman kanta, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya bada tabbacin hukumar za ta gudanar da sahihin zabe.
A cewarsa, hukumar ta kawo katin zabe na farko na masu kada kuri’a don gudu masu zarge-zarge da kuma kin amincewa.
Ya kuma kara da cewa an kuma dauki matakin saukakawa kada kuri’a a tsakanin nakasassu.
