Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jigawa Ta Gargadi ‘Yan Fansho Da Masu Shirin Ritaya

Gwamnatin jihar Jigawa ta gargadi ma’aikatan gwamnati da ke shirin yin ritaya da su yi taka-tsan-tsan da masu yin sojan gona. Kamar yadda Daily Post ta ruwiato.

Sakataren zartarwa na hukumar fansho a jihar Jigawa Alhaji Kamilu Aliyu Musa ne ya yi wannan gargadin a wajen biyan sama da Naira biliyan daya ga ma’aikatan gwamnati 474 da za su yi ritaya a watan Oktoban 2023.

Ya ce an bullo da shirin ne domin tabbatar da tsarin bayar da gudunmawar fansho mai dorewa, don haka babu wani dalili na neman kudi daga duk wanda zai yi ritaya kafin yasami hakkokinsa.

“Manufar shirin ita ce tabbatar da tsarin bayar da gudunmawar fansho mai dorewa wanda zai tabbatar da biyan bukatun ma’aikatan da suka yi ritaya cikin gaggawa a jihar Jigawa. Ba kwa buƙatar biyan kobo ga kowa kafin samun kudadenku na ritayar ku,” in ji shi.

A cewarsa, hukumar ta samu rahotannin yadda wasu mutane ke karbar kudade daga ma’aikatan gwamnati da za su yi ritaya domin biyan bukatunsu.

Don haka Kamilu ya gargadi ma’aikatan gwamnati da su yi hattara da masu damfara tare da kai rahoto ga hukumar tsaro mafi kusa domin daukar matakin da ya dace.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet