Kasuwanci
Gwamna El-rufa’i Ya Bukaci Gwamnatin Buhari Ta Gaggauta Cire Tallafin Mai
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta cire tallafin man fetur.
El-Rufai ya yi wannan kiran ne a taron jihohi na NESG, wanda ya gudana jiya a Abuja.
Da aka tambaye shi yayin zaman cewa me ya kamata gwamnati ta sa gaba, gwamnan ya ce, “a cire tallafin man fetur nan take.
Gwamnan ya ce takwarorinsa na Najeriya sun amince a cire tallafin man fetur a watan Satumba na 2021.
El-Rufai ya ce: “A karkashin wannan gwamnatin, kusan duk wata muna haduwa ta aiki, domin tattalin arzikinmu daya ne kawai.
”Mun dauki matakin cire tallafin a watan Satumba na 2021 kuma Ministar kudi ta amince da bukatar mu.”
Kalaman El-Rufai na zuwa ne a daidai lokacin da farashin Man Fetur, PMS, ya tashi zuwa N190/kowace lita daga N165/kowace lita a Abuja.
